Isaiah 55:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Don me za ku kashe kuɗi a kan abin da ba abinci ba, ku kuma yi wahala a kan abin da ba za ku ƙoshi ba? Ku saurara, ku saurare ni, ku kuma ci abin da yake da kyau, ranku kuma zai ji daɗin abinci mafi kyau.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُوانْمٜىٰ كُكٜىٰ كَشٜىٰ كُطِ عَكَنْ أَبِنْدَ بَ عَبِنْثِبَ؟ دُوانْمٜىٰ كُمَ كُنَ كَشٜىٰ كُطِنْ عَيْكِنْكُ عَكَنْ أَبِنْدَ بَيْ بِيَ بُڧَاتَبَ؟ كُجِنِ دَݣَوْ، كُثِ عَبِنْثِ مَيْݣَوْ، كُجِ وَ رَنْكُ دَاطِے دَ عَبِنْثِ مَڢِے ݣَوْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Don me za ku kashe kuɗi a kan abin da ba abinci ba? Don me za ku ɓad da albashinku, amma kuna ta shan yunwa? Ku kasa kunne gare ni, ku yi abin da na faɗa, Za ku sha daɗin abinci mafi kyau duka.