Isaiah 55:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bari mugu ya bar irin halinsa mugu kuma ya sāke irin tunaninsa. Bari yă juyo ga Ubangiji, zai kuwa ji tausayinsa, ya juyo ga Allahnmu kuma, gama shi mai gafartawa ne a sauƙaƙe.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَرِ مَيْ مُغُنْتَا يَبَرْ حَنْيَرْسَ، مَرَرْ أَدَلْثِے كُمَ يَبَرْ تُنَانِنْسَ؞ بَرِ يَكُواْمُواْ غَ يَهْوٜىٰهْ ، شِيكُوَ ذَيْ يِمَسَ جِنْڧَيْ، يَكُواْمُواْ غَ يَهْوٜىٰهْ غَمَا أَشِرْيٜىٰ يَكٜىٰ يَغَاڢَرْثٜىٰ شِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bari mugaye su bar irin al'amuransu, Su sāke irin tunaninsu. Bari su juyo wurin Ubangiji, Allahnmu, Shi mai jinƙai ne, mai saurin gafartawa.