Isaiah 57:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da kuka nemi taimako, bari tarin gumakanku su cece ku! Iska za tă kwashe dukansu tă tafi, ɗan numfashi kawai zai hura su. Amma mutumin da ya mai da ni mafakarsa zai gāji ƙasar ya kuma mallaki dutsena mai tsarki.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ كِكَيِ كُوكَنْ نٜىٰمَنْ تَيْمَكُواْ، بَرِ غُمَكَنْ دَ كِكَ تَتَّارَ سُكُٻُتَرْ دَكٜىٰ؞ إِسْكَ ذَاتَ ݣُوشٜىٰسُ تَتَڢِے دَسُو، نُمْڢَشِ كُمَ يَكَوَرْ دَسُو؞ عَمَّا دُكْ وَنْدَ يَدُواْغَرَ غَرٜىٰنِ، ذَيْ غَاجِ ڧَسَرْ، يَكُمَ مَلَّكِ تُدُنَ مَيْ ڟَرْكِے؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da kuka ta da murya kuka yi kuka, to, bari tattaruwar gumakanku su cece ku! Iska za ta fauce su, numfashi zai kawar da su. Amma wanda ya fake gare ni zai mallaki ƙasar. Zai kuma yi sujada a Haikalina.”