Isaiah 57:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kuna cike da muguwar sha’awa mai ƙonawa a cikin itatuwan oak da kuma a ƙarƙashin kowane itace mai inuwa; kuna miƙa hadayar ’ya’yanku a rafuffuka da kuma a ƙarƙashin tsagaggun duwatsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُوغُوَرْ شَعَوَرْكُ تَكَيْكُ غَ يِنْ لَلَتَ أَوُرِنْ سُجَّدَ ڟَكَانِنْ عِتَتُوَ مَرَسَ بُوشٜىٰوَ، دَ ڧَرْڧَشِنْ كُواْوَنٜىٰ إِتَاثٜىٰ مَيْ بَادَ إِنُوَ؞ كُنَ كَكَّشٜىٰ یَیَنْكُ عَثِكِنْ ݣُورِ، دَ ثِكِنْ مَڢَكَا أَ مَنْيَنْ دُوَڟُو؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ku da muguwar sha'awa take ƙonawa a tsakanin itatuwan oak, da ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa. Ku da kuka karkashe 'ya'yanku a cikin kwaruruka, da a ƙarƙashin duwatsu masu tsayi?