Isaiah 6:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A bisansa akwai serafofi, kowanne yana da fikafikai shida. Fikafikai biyu sun rufe fuskokinsu, da biyu suka rufe ƙafafunsu, biyu kuma da su suke tashi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَݣَويْ حَلِتُّو مَاسُ كَمَ دَ هَرْشٜىٰنْ وُتَا عَبِسَنْسَ، كُواْوَنّٜىٰنْسُ يَنَدَ ڢِكَڢِكَيْ شِدَ؞ دَ ڢِكَڢِكَيْ بِيُ سُنَ رُڢٜىٰ ڢُسْكُواْكِنْسُ دَ بِيُ كُمَ سُنَ رُڢٜىٰ جِكِنْسُ دَ سَوْرَنْ بِيُنْ كُمَ سُنَ تَاشِ سَمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kewaye da shi sai ga waɗansu talikai masu kama da harshen wuta a tsaye, ko wannensu yana da fikafikai shida. Ko wannensu ya rufe fuskarsa da fiffike biyu, jikinsa kuma da fiffike biyu, sauran fiffike biyu ɗin kuma, da su yake tashi.