Isaiah 60:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ƙofofinki kullum za su kasance a buɗe, ba za a ƙara rufe su da rana ko da dare ba, saboda mutane su kawo miki dukiyar al’ummai, sarakunansu za su kasance a gaba a jerin gwanon nasara.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڧُواْڢُواْڢِنْكِ ذَاسُ كَسَنْثٜىٰ عَبُوطٜىٰ كُلُّمْ، دَرٜىٰ دَ رَانَ بَذَاعَ رُڢٜىٰسُبَ، دُواْمِنْ أَلْعُمَّيْ سُيِ تَكَٰوُاْ مِكِ أَرْزِڧِنْسُ، سَرَاكُنَنْسُ سُيِ جٜىٰرِنْ ڠُونُواْ ذُوَا وُرِنْكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ƙofofinki za su kasance a buɗe dare da rana, Domin sarakunan al'ummai su kawo miki dukiyarsu.