Isaiah 60:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan dukan mutanenki za su zama masu adalci za su kuma mallaki ƙasar har abada. Su ne reshen da na shuka, aikin hannuwana, don nuna darajata.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكَنْ مُتَنٜىٰنْكِ ذَاسُ ذَمَ مَاسُ أَدَلْثِے، ذَاسُ كُوَ غَاجِ سُومَلَّكِ ڧَسَرْ حَرْ أَبَدَا؞ جَمَعَتَ رٜىٰشٜىٰ نٜىٰ وَنْدَ نَدَسَ، عَيْكِنْ حَنُّوَنَ نٜىٰ دُواْمِنْ عَبَيَّنَ دَرَجَتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dukan mutanenki za su yi abin da yake daidai, Za su kuwa mallaki ƙasar har abada. Ni na dasa su, ni na yi su Domin su bayyana girmana ga duka.