Isaiah 60:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mafi ƙanƙanta a cikinki za tă zama dubu, ƙarami zai zama al’umma mai girma. Ni ne Ubangiji, cikin lokacinsa zan yi haka da sauri.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِيَلِ نَڧَرْشٜىٰ عَثِكِنْكِ ذَيْ ذَمَ ذُرِيَ، مَڢِے ڧَنْڧَنْتَ عَثِكِنْكِ كُمَ ذَيْ ذَمَ أَلْعُمَّ مَيْ ڧَرْڢِے؞ نِے يَهْوٜىٰهْ نٜىٰ، دَ سَوْرِ ذَنْسَا وَنَّنْ يَثِكَ أَدَيْدَيْ لُواْكَثِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Har ma da iyalin da suka fi ƙanƙanta da ƙasƙanci, Za su zama babbar al'umma, Kamar al'umma mai iko. Zan sa wannan ya faru nan da nan Sa'ad da lokacin da ya dace ya yi. Ni ne Ubangiji!”