Isaiah 60:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ki ɗaga idanunki ki duba kewaye da ke. Duka sun tattaru suka kuma zo wurinki; ’ya’yanki maza daga nesa, ana kuma ɗaukan ’ya’yanki mata a hannu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«طَغَ عِدَنُونْكِ، كِدُوبَ كٜىٰوَيٜىٰ، كِغَنِ، مُتَنٜىٰنْكِ سُنَ تَتَّارُوَ، سُنَ ذُوَا وُرِنْكِ؞ غَا یَیَنْكِ مَظَا سُنَ ذُوَا دَغَ نٜىٰسَ، یَیَنْكِ مَتَ كُمَ أَنَ رِڧٜىٰ دَسُو أَ حَنُّ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ki duba kewaye da ke, ki ga abin da yake faruwa, Mutanenki suna ta tattaruwa domin su komo gida! 'Ya'yanki maza za su taho daga nesa, Za a ɗauki 'ya'yanki mata kamar yara.