Isaiah 61:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ina jin daɗi ƙwarai a cikin Ubangiji; raina yana farin ciki a cikin Allahna. Gama ya suturce ni da rigunan ceto ya yi mini ado da rigar adalci, yadda ango yakan yi wa kansa ado kamar firist kamar kuma yadda amarya takan sha ado da duwatsunta masu daraja.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِنَ يِنْ ڢَضٍ ثِكِ مَيْ يَوَ سَبُواْدَ أَبِنْدَ يَهْوٜىٰهْ يَيِ، ذُوثِيَاتَ تَنَدَ ڢَضٍ ثِكِ سَبُواْدَ اللَّهْ نَا؞ غَمَا يَسَا مِنِ رِغَرْ ثٜىٰتُواْ، يَرُڢٜىٰنِ دَ رِيغُنَنْ أَدَلْثِے، كَمَرْ يَدَّ أَنْغُواْ يَكَنْيِ أَدُواْ دَ هُولَرْ ڢِرِسْتِ، كَمَرْ يَدَّ أَمَرْيَ تَكَنْيِ أَدُواْ دَ كَايَ مَاسُ وَلْڧِيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Urushalima tana murna saboda abin da Ubangiji ya yi. Tana kama da amaryar da ta sha ado a ranar aurenta. Allah ya suturce ta da ceto da nasara.