Isaiah 61:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona, in maido musu rawani mai kyau a maimako na toka, man murna a maimako na makoki, da kuma rigar yabo a maimako na ruhun fid da zuciya. Za a ce da su itatuwan oak na adalci, shukin Ubangiji don bayyana darajarsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِنْ تَعَظَنْتَرْدَ مَاسُ بَڧِنْ ثِكِ أَ سِهِيُواْنَ، إِنْبَاسُ هُولَرْ ڢَضٍ ثِكِ مَيْ أَدُواْ مَيْمَكُوانْ ظُبَ تُواْكَ عَكَيْ، مَنْ نُونَ مُرْنَ مَيْمَكُوانْ بَڧِنْ ثِكِ، رِغَرْ وَاڧَرْ يَبُواْ مَيْمَكُوانْ ڢِدَّ ذُوثِيَا؞ ذَاسُ كَڢُ ثِكِنْ أَدَلْثِے كَمَرْ إِتَاثٜىٰ مَيْ ڧَرْڢِے، شُوكَرْ دَ يَهْوٜىٰهْ يَيِ دُواْمِنْ عَبَيَّنَ دَرَجَرْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Domin in kawo wa masu makoki a Sihiyona Farin ciki da murna maimakon baƙin ciki, Waƙar yabo maimakon ɓacin rai. Ubangiji kansa zai lura da su, Za su ji daɗi kamar itace mai duhuwa. Kowa da kowa zai aikata abin da yake daidai, Za a yi yabon Allah saboda abin da ya yi.