Isaiah 61:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A maimakon kunyarsu mutanena za su sami rabi riɓi biyu, a maimakon wulaƙanci za su yi farin ciki cikin gādonsu; ta haka za su gāji rabo riɓi biyu a ƙasarsu, da kuma madawwamin farin ciki zai zama nasu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مَيْمَكُوانْ كُنْيَا، ذَاكُ سَامِ دَرَجَ؞ مَيْمَكُوانْ رٜىٰنِ، ذَاكُيِ ڢَضٍ ثِكِنْ غَادُوانْكُ؞ مَلَّكَرْكُ ذَيْ يَلْوَتَ، ڢَضٍ ثِكِنْكُ كُمَ حَرْ أَبَدَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kunyarku da shan wulakancinku za su ƙare. Za ku zauna a ƙasarku, Za a riɓanya dukiyarku, Za ku yi ta farin ciki har abada.