Isaiah 62:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji ya rantse da hannunsa na dama ta hannunsa kuma mai iko cewa, “Ba zan ƙara ba da hatsinki ya zama abinci ga abokan gābanki ba, baƙi kuma ba za su ƙara shan ruwan inabin wanda kika sha wahala samu ba;
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهْوٜىٰهْ يَا طَغَ حَنُّنْسَ مَيْ إِيكُواْ يَايِ ضَنْڟُوَا، «بَذَنْ سَاكٜىٰ بَ أَبُواْكَنْ غَابَنْكِ حَڟِنْكِ يَذَمَ عَبِنْثِنْسُبَ؞ بَاڧِ بَذَاسُ ڧَارَ شَنْ ضُوً إِنَبِنْكِ وَنْدَ كِكَيِ ڢَامَرْ عَيْكِنْسَبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji ya yi alkawari mai ƙarfi, Ta wurin ikonsa kuwa zai cika shi. “Hatsinku ba zai ƙara zama abincin abokan gābanku ba, Baƙi ba za su ƙara shanye ruwan inabinku ba.