Isaiah 63:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan mutanensa suka tuna kwanakin dā, kwanakin Musa da mutanensa, ina yake shi wanda ya fitar da su ta teku, da makiyayan garkensa? Ina shi yake wanda ya sa Ruhunsa Mai Tsarki a cikinsu,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ جَمَعَرْسَ سُكَ تُنَ دَ ݣُونَكِنْ دَا، سُكَ تُنَ دَ زَامَانِنْ مُوسَٰى بَاوَنْسَ؞ إِنَا يَهْوٜىٰهْ يَكٜىٰ وَنْدَ يَبِيدَسُو تَثِكِنْ تٜىٰكُ، تَرٜىٰدَ مَكِيَايِنْ جَمَعَرْسَ؟ إِنَا شِے يَكٜىٰ وَنْدَ يَسَا رُوحُنْسَ مَيْ ڟَرْكِے يَكَسَنْثٜىٰ أَڟَكِيَرْ جَمَعَرْسَ؟
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma suka tuna da zamanin dā, zamanin Musa bawan Ubangiji, suka yi tambaya suka ce, “Yanzu fa, ina Ubangiji yake wanda ya ceci shugabannin jama'arsa daga teku? Ina Ubangiji yake, wanda ya ba Musa iko musamman?