Isaiah 65:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “Bayin za su ci, amma ku za ku ji yunwa; bayina za su sha, amma ku za ku ji ƙishi; bayina za su yi farin ciki amma ku za ku sha kunya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«سَبُواْدَ حَكَ،» إِنْجِ عُبَنْغِجِ يَهْوٜىٰهْ ، «بَايِنَ ذَاسُثِ، عَمَّا كُو ذَاكُ ذَوْنَ دَ يُنْوَ؞ بَايِنَ ذَاسُ شَا، عَمَّا كُو ذَاكُ ذَوْنَ دَ ڧِشِ؞ بَايِنَ ذَاسُيِ ڢَضٍ ثِكِ، عَمَّا كُو ذَاكُشَا كُنْيَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Saboda haka ina faɗa muku, cewa su waɗanda suke yin sujada gare ni suna kuwa yi mini biyayya, za su sami wadataccen abinci da abin sha, amma ku za ku sha yunwa da ƙishi. Su za su yi murna, amma ku za ku sha kunya.