Isaiah 65:25 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kyarketai da ’yan raguna za su ci abinci tare, zaki kuma zai ci buɗu kamar yadda shanu suke yi, amma ƙura ce za tă zama abincin maciji. Ba za su ƙara cuci ko su yi ɓarna a kan dukan dutsena mai tsarki ba,” in ji Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ݣَرْكٜىٰثِ دَ طَنْ ضَغُواْ ذَاسُثِ عَبِنْثِ تَرٜىٰ، ذَاكِ ذَيْثِ ثِيَوَ كَمَرْ سَانِيَ، عَمَّا مَثِيجِ، عَبِنْثِنْسَ ڧُورَرْ ڧَسَا نٜىٰ كَوَيْ؞ بَابُ أَبِنْدَ ذَيْ ثُوتَرْ كُواْ يَهَلَّكَ وَنِ، عَكَنْ دُكَنْ سِهِيُواْنَ تُدُنَ مَيْ ڟَرْكِے؞ نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kyarketai da 'yan raguna za su ci abinci tare, zaki kuma zai ci budu kamar yadda shanu suke yi. Maciji ba zai ƙara zama abu mai hatsari ba. A kan Sihiyona tsattsarkan dutsena, ba za a sami wani abu da zai cutar ba, ko wani mugun abu.”