Isaiah 65:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
suna cewa, ‘Ku tsaya a can; kada ku yi kusa da ni, gama na fi ku tsarki!’ Irin mutanen nan hayaƙi ne a hancina, wuta kuma da take cin gaba da ci dukan yini.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَ مُتَنٜىٰنْ دَسُكٜىٰثٜىٰوَ ‹كَدَ كَذُواْ كُسَ، كَيِ نٜىٰسَ دَنِے غَمَا أَنْكٜىٰٻٜىٰنِ دَ ڟَرْكِے؞› إِرِنْ مُتَنٜىٰنَّنْ كَمَرْ هَيَاڧِے مَيْ وَرِ نٜىٰ أَهَنْثِنَ، سُنْسَا ڢُشِنَ يَيِتَثِ كَمَرْ وُتَا دُكَنْ يِنِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan su riƙa ce wa sauran mutane, ‘Ku yi nesa da mu gama muna da tsarki da yawa, har da ba za mu taɓa ku ba.’ Ba zan daure da irin waɗannan mutane ba, fushina a kansu kamar wuta ce wadda ba za ta taɓa mutuwa ba.