Isaiah 65:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kamar sa’ad da ruwan ’ya’yan itace yana samuwa a cikin tarin ’ya’yan inabi mutane kuma su ce, ‘Kada a lalace shi, har yanzu akwai abu mai kyau a ciki,’ haka nan zan yi a madadin bayina; ba zan hallaka su duka ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞ تُنْدَيَكٜىٰ عَثِكِنْ ڧُنْشِنْ یَیَنْ إِنَبِے أَݣَويْ یَیَ مَاسُ ݣَوْ، بَذَاعَ ظُبَرْدَ ڧُنْشِنْ طُنْغُمْبَ، غَمَا أَݣَويْ أَلْبَرْكَ عَثِكِ؞ حَكَكُمَ تُنْدَيَكٜىٰ عَثِكِنْ جَمَعَتَ أَݣَويْ بَايِ مَاسُ أَمِنْثِ، بَذَنْ هَلَّكَ جَمَعَ دُكَبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji ya ce, “Ba wanda ya lalatar da 'ya'yan inabi, maimakon haka sai suka yi ruwan inabi da su. Ni kuwa ba zan hallakar da dukan mutanena ba, zan ceci waɗanda suke bauta mini.