Isaiah 66:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Waɗanda suka tsarkake suka kuma tsabtacce kansu don su je lambu, suna bin wannan da yake tsakiya waɗannan da suke cin naman aladu da ɓeraye da waɗansu abubuwan banƙyama, za su sadu da ƙarshensu tare,” in ji Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ «ڧَرْشٜىٰ يَيِ كُسَ دُواْمِنْ وَطَنْدَ سُكَ ڟَبْتَثٜىٰ كَنْسُ دُواْمِنْ يِنْ سُجَّدَ غَ غُمَكَ أَغُواْنَكِنْسُ، دُواْمِنْ كُمَ وَطَنْدَ سُكَيِ جٜىٰرِنْ ڠُونُواْ ذُوَا وُرِنْ دَسُكٜىٰ ثِنْ نَامَنْ أَلَدٜىٰ دَ نَٻٜىٰرَ دَ نَسَوْرَنْ أَبُبُوَ مَاسُ بَنْ ڨَمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji ya ce, “Ƙarshe ya kusa ga waɗanda suka tsabtace kansu domin sujadar arna, suka kuma yi jerin gwano zuwa ɗakin tsafi a lambu, inda suka ci naman alade da na ɓera, da waɗansu abinci masu banƙyama.