Isaiah 66:20 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Za su kuma dawo da dukan ’yan’uwanku, daga dukan al’ummai, zuwa dutsena mai tsarki a Urushalima kamar hadaya ga Ubangiji, a kan dawakai, a kekunan yaƙi da wagonu, da kuma a kan alfadarai da kuma raƙuma,” in ji Ubangiji. “Za su kawo su, kamar yadda Isra’ilawa suke kawo hadayun hatsi, zuwa haikalin Ubangiji a cikin tsabtatattun kore.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاعَكَٰوُاْ دُكَنْ یَنْعُوَنْكُ دَغَ ثِكِنْ دُكَنْ أَلْعُمَّيْ، أَ مِيڧَ مِنِسُ ݣَوْتَا؞ ذَاعَكَٰوُاْسُ عَبَبَّنْ تُدُنَ مَيْ ڟَرْكِے، وَتُواْ عُرُوشَلِيمَ؞ ذَاعَكَٰوُاْسُ عَكَنْ دَوَكِ دَ جَاكُنَ دَ رَاڧُمَ دَ كٜىٰكُنَنْ دُواْكِ دَ كٜىٰكُنَنْ شَانُو كَمَرْ يَدَّ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا سُكٜىٰ كَٰوُاْ هَدَايَ ثِكِنْ ݣُونُواْ مَيْ ڟَبْتَ عَثِكِنْ غِدَانَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za su taho da 'yan ƙasarku daga al'ummai, su kawo mini su kyauta. Za su zo da su a tsattsarkan dutsena, wato Urushalima, za su kawo su a kan dawakai, da alfadarai, da raƙuma, da cikin karusai, kamar dai yadda Isra'ilawa suke kawo hadaya ta hatsi a Haikali cikin tsabtatattun ƙore.