Isaiah 66:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
saboda haka ni ma zan aukar musu da masifa mai zafi in kuma kawo musu abin da suke tsoro. Gama sa’ad da na yi kira, ba wanda ya amsa, sa’ad da na yi magana, ba wanda ya saurara, Sun aikata mugunta a idona suka kuma zaɓa abin da ba na jin daɗi.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نِے مَا ذَنْ ذَاٻِ بِنْ رَعَيِنَ إِنْ أَوْكَرْ مُسُ دَ مَسِيڢَ، إِنْ كَٰوُاْ مُسُ أَبِنْدَ سُكٜىٰ جِنْ ڟُواْرُوانْسَ؞ غَمَا دَ نَيِ كِرَا، بَابُوَنْدَ يَأَمْسَ، دَ نَيِ مَغَنَ، بَابُوَنْدَ يَسَوْرَرَ؞ عَمَّا سُكَ عَيْكَتَ مُغُنْتَا أَعِدَنُونَ، سُكَ ذَاٻَا سُيِ أَبِنْدَ بَنْ جِ دَاطِنْسَبَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Saboda haka zan aukar musu da masifa, ainihin abin da suke jin tsoro, gama ba wanda ya amsa sa'ad da na yi kira, ko ya kasa kunne sa'ad da na yi magana. Suka zaɓa su yi mini rashin biyayya, su kuma aikata mugunta.”