Isaiah 66:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wa ya taɓa jin irin wannan abu? Wa ya taɓa gani irin abubuwan nan? Za a iya ƙirƙiro ƙasa a rana ɗaya ko a haifi al’umma farat ɗaya? Duk da haka da zarar Sihiyona ta fara naƙuda sai ta haifi ’ya’yanta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَ يَتَٻَ جِنْ إِرِنْ وَنَّنْ؟ وَ يَتَٻَ غَنِنْ إِرِنْ وَنَّنْ؟ ذَاعَ عِيَ حَيْڢَرْ دَ جَمَعَ أَ رَانَ طَيَ نٜىٰ؟ كُواْ ذَاعَ عِيَ حَيْڢَرْ دَ أَلْعُمَّ نَنْ دَنَنْ؟ عَمَّا دَظَرَرْ سِهِيُواْنَ تَڢَارَ نَڧُدَ، سَيْ تَحَيْڢِ یَیَنْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ko akwai wanda ya taɓa gani ko ya ji labari irin wannan abu? Ko an taɓa haihuwar al'umma rana ɗaya? Sihiyona ba za ta sha wahala ba kafin a haifi al'umma.