Isaiah 7:20 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A wannan rana Ubangiji zai yi amfani da rezan da aka yi haya daga ƙetaren Kogi, sarkin Assuriya ke nan, yă aske kanku da gashin ƙafafunku, zai kuma aske gemunku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«أَ رَانَرْ نَنْ عُبَنْ‌غِجِ ذَيْ يِ هَيَرْ سَرْكِنْ أَسُّرِيَ دَغَ ڧٜىٰتَرٜىٰنْ كُواْغِنْ يُڢِرٜىٰتِسْ، ذَيْ يِ أَمْڢَانِ دَشِ كَمَرْ رٜىٰظَ، يَيِ مُكُ أَسْكِ دَغَ كَيْ دَ غٜىٰمُ دَ دُكَنْ غَاشِنْ جِكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“A lokacin nan, Ubangiji zai yi ijara da wanzami daga wancan hayi na Yufiretis, wato Sarkin Assuriya! Zai aske gyammanku, da gashin kawunanku, da na jikunanku.