Isaiah 7:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kuma saboda yalwa madarar da suke bayarwa, zai kasance da madarar da zai sha. Dukan waɗanda suka rage a ƙasar za su sha madara da zuma.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا ذَاسُ بَادَ مَدَرَ عَيَلْوَثٜىٰ ڢِيٜىٰدَ يَدَّ عَكٜىٰسُواْ؞ غَمَا دُكَنْ وَطَنْدَ سُكَ رَغُ عَڧَسَرْ ذَاسُدِنْ‌غَ شَنْ مَدَرَ دَ ضُوً ظُمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
za su ba da isasshiyar madarar da za ta biya dukan bukatarsa. Hakika dukan waɗanda suka ragu a ƙasar za su sami yawan albarka su ƙoshi.