Isaiah 7:24 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mutane za su je can da baka da kibiyoyi, gama ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne za su rufe ƙasar.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاعَجٜىٰ ڢَرَوْتَ أَوُرِنْ تَرٜىٰدَ بَكَ دَ كِبِيُواْيِ، غَمَا دُكَنْ ڧَسَرْ ذَاتَ ذَمَ ڧَيُواْيِ دَ وُتَا وُتَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba wanda yake da ƙarfin hali da zai iya tafiya can, sai ko wanda yake da kwari da baka. Hakika ƙasar duka za ta cika da sarƙaƙƙiya da ƙayayuwa.