Isaiah 8:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Cikin matsuwa da yunwa, za su yi ta kai komo ko’ina a ƙasar; sa’ad da suka ji yunwa, za su yi fushi su tā da idanu sama, su zagi sarkinsu da Allahnsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاسُيِ تَيَٰوُاْ عَڧَسَرْ ثِكِنْ عَذَابَ دَ يُنْوَ؞ ذَيْ كُوَ كَسَنْثٜىٰ ثٜىٰوَ عَثِكِنْ يُنْوَرْسُ ذَاسُيِ ڢُشِے سُواْسَيْ حَرْ سُلَعَنْثِ سَرْكِنْسُ دَ أَلُّواْلِنْسُ؞ ذَاسُ كُوَ جُويَرْدَ ڢُسْكُواْكِنْسُ سُدُوبِے سَمَ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mutane za su yi ta kai da kawowa a ko'ina cikin ƙasar, cikin matsuwa da yunwa. A yunwar da suke sha da haushin da suke ji, za su zagi sarkinsu, su kuma zagi Allahnsu. Har ma zai yiwu su ɗaga ido su dubi sararin sama,