Isaiah 8:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
saboda haka Ubangiji yana shirin yă kawo musu rigyawar ruwan Kogi, wato, sarkin Assuriya da dukan sojojinsa. Zai cika dukan gaɓoɓinsa, yă kuma malala har zuwa bakin kogi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تُواْ، غَاشِ ذَنْ عَيْكُواْ مُسُ دَ ضُوً بَبَّنْ كُواْغِنَّنْ مَيْ ڧَرْڢِے، وَتُواْ سَرْكِنْ أَسُّرِيَ دَ دُكَنْ سُواْجُواْجِنْسَ؞ ذَيْ تَاشِ كَمَرْ بَبَّنْ كُواْغِنَّنْ يُڢِرٜىٰتِسْ، يَثِثِّكَ كُواْعِنَ يَذَمَ أَمْبَلِيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ni Ubangiji kuwa, zan kawo Sarkin Assuriya da dukan sojojinsa su fāɗa wa Yahuza. Za su tasar musu kamar rigyawar Kogin Yufiretis wadda ta yi ambaliya ta shafe kowace gaɓa.