Isaiah 9:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Arameyawa daga gabas da Filistiyawa daga yamma sun cinye Isra’ila da buɗaɗɗen baki. Duk da haka, fushinsa bai huce ba, hannunsa har yanzu yana a miƙe.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُرِيَاوَا أَبُواْكَنْ غَابَنْسُ دَغَ غَبَسْ دَ ڢِلِسْتِيَاوَا دَغَ يَمَّ سُنْ بُوطٜىٰ بَاكِنْسُ دُواْمِنْ سُثِنْيٜىٰ إِسْرَٰٓءِيلَ؞ دُكْ دَ وَنَّنْ، ڢُشِنْ يَهْوٜىٰهْ يَا ڧِ يَݣُونْتَ، حَنُّنْ حُكُنْثِنْسَ يأَنَانً أَ مِيڧٜىٰ!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suriya daga gabas, da Filistiya daga yamma, sun wage bakinsu don su haɗiye Isra'ila. Duk da haka fushin Ubangiji bai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.