Isaiah 9:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Tabbatacce mugunta tana ƙuna kamar wuta; tana cin ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya, ta sa wuta a jeji mai itatuwa masu yawa, don yă yi murtuke hayaƙi har zuwa sama.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
حَڧِيڧَ مُغُنْتَا تَنَ تَڧُواْنَ كَمَرْ وُتَا، تَنَ ثِنْ ڧَيُواْيِ دَ وُتَا وُتَا؞ تَنَ ڧُواْنٜىٰ دَاجِ دَ كُرْمِ، ڧُنْشِنْ هَيَاڧِنْ وُتَرْ يَنَ تَاشِ سَمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Muguntar jama'a tana ci kamar wutar da take cinye ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya. Tana ci kamar wutar dawa wadda hayaƙinta take murtukewa har sama.