Isaiah 9:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Manasse zai mai da Efraim abinci, Efraim kuma yă cinye Manasse; tare za su yi gāba da Yahuda. Duk da haka, fushinsa bai huce ba, hannunsa har yanzu yana a miƙe.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْ مَنَسّٜىٰ سُنْثِنْيٜىٰ نَ إِڢْرَيِمْ، مُتَنٜىٰنْ إِڢْرَيِمْ كُمَ سُنْثِنْيٜىٰ نَ مَنَسّٜىٰ، تَرٜىٰ كُمَ سُنْيِ غَابَادَ مُتَنٜىٰنْ يَهُودَ؞ دُكْ دَ وَنَّنْ، ڢُشِنْ يَهْوٜىٰهْ يَڧِ يَݣُونْتَ، حَنُّنْ حُكُنْثِنْسَ يأَنَانً أَ مِيڧٜىٰ!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Jama'ar Manassa da jama'ar Ifraimu suna fāɗa wa juna, tare kuma suke fāɗa wa Yahuza. Duk da haka fushin Ubangiji bai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.