James 2:25 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ta haka kuma ashe, Rahab karuwan nan ba a ɗauke ta mai adalci ce saboda abin da ta yi ba ne sa’ad da ta ba wa ’yan leƙen asirin nan masauƙi ta kuma sallame su suka tafi ta wata hanya dabam?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
حَكَ يَكٜىٰ كُمَ دَ كَارُوَرْ نَنْ رَهَبْ أَ لُواْكَثِنْ دَ تَٻُواْيٜىٰ یَنْ لٜىٰڧٜىٰنْ أَسِيرِنْ ڧَسَرْ نَنْ، تَكُمَ تَيْمَكٜىٰسُ سُنْ ڟِيرَا تَوَتَ حَنْيَ دَبَمْ؞ بَتَوُرِنْ أَيُّكَ نٜىٰ تَذَمَ مَرَرْ لَيْڢِے بَ؟
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ashe, ba haka kuma Rahab karuwar nan ta sami kuɓuta saboda aikatawarta ba? Wato, sa'ad da ta sauki jakadun nan, ta fitar da su ta wata hanya dabam?