James 2:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
in kuka mai da hankali na musamman ga mutumin da yake da riguna masu tsadan nan kuka kuma ce, “Ga wurin zama mai kyau dominka,” amma kuka ce wa matalaucin nan, “Kai tsaya daga can,” ko kuwa, “Ka zauna a ƙasa kusa da ƙafafuna,”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِدَنْ ذَاكُڢِبَا مَيْ أَرْزِڧِنَّنْ غِرْمَ كُثٜىٰ مَسَ «غَا كُجٜىٰرَ مَيْݣَوْ كَذَوْنَ،» عَمَّا كُثٜىٰ وَمَتَلَوْثِنَّنْ «كَڟَيَ عَثَنْ،» كُواْ كُمَ «كَذَوْنَ عَڧَسَا،»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
sa'an nan kuka kula da mai tufafi masu ƙawar nan, har kuka ce masa, “Ga mazauni mai kyau a nan,” matalaucin nan kuwa kuka ce masa, “Tsaya daga can,” ko kuwa, “Zauna a nan ƙasa a gabana,”