James 3:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ko kuwa misali, mu dubi jiragen ruwa, mana. Ko da yake suna da girma ƙwarai kuma iska mai ƙarfi ce take tura su, ana tuƙa su da ɗan ƙaramin sandan ƙarfe ne zuwa duk inda mai tuƙin jirgin yake so.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُكُمَ دُوبَ جِضَاغٜىٰنْ ضُوَ كُغَانٜىٰ؞ كُواْدَيَكٜىٰ سُو مَنْيَنٜىٰ، كُمَ إِسْكَ مَيْ ڧَرْڢِثٜىٰ تَكٜىٰ تُورَسُ، دُكْدَهَكَ دَ طَنْ ڧَرَمِنْ سَنْدَنْ تُوڧِ نٜىٰ مَيْ تُوڧِنْ جِضْغٍ يَكَنْ عِيَ جُويَ جِضْغٍ ذُوَا كُواْعِنَ دَ يَكٜىٰسُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ku dubi jiragen ruwa kuma, ko da yake suna da girma haka ƙaƙƙarfar iska kuma tana kora su, duk da haka, da ɗan ƙaramin ƙarfe ne matuƙi yake juya su duk inda ya nufa.