James 5:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka ’yan’uwa, sai ku yi haƙuri har dawowar Ubangiji. Ku dubi yadda manomi yakan jira gona ta ba da amfaninta mai kyau, da kuma yadda yake haƙurin jiran ruwan sama na damina da na kaka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ وَنَّنْ، یَنْعُوَ، كُيِ ذَمَنْ حَڧُرِ حَرْ سَيْ عُبَنْ‌غِجِ يَدَاوُاْ؞ كُدُوبِے إِرِنْ حَڧُرِنْ دَ مَنُواْمِ يَكَنْيِ لُواْكَثِنْ دَيَكٜىٰ جِرَا غُواْنَرْسَ تَبَادَ أَمْڢَانِ مَيْݣَوْ؞ دَ يَوَنْ حَڧُرِ يَكَنْ جِرَا ضُوً شُوكَ دَ ضُوً ڧَرْشٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Domin haka, sai ku yi haƙuri, 'yan'uwana, har ya zuwa ranar komowar Ubangiji. Ga shi, manomi yana sa rai ga samun amfanin gona mai albarka, yana kuwa haƙuri da samunsa, har a yi ruwan shuka da na kaka.