Jeremiah 1:16 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zan furta hukunci a kan mutanena saboda muguntarsu na yashe ni, suna ƙona turare ga waɗansu alloli suna kuma bauta wa abin da hannuwansu suka yi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَنْ سَنَرْدَ شَرِيعَتَ تَغَابَدَ مُتَنٜىٰنَ سَبُواْدَ مُغُنْتَارْسُ تَڧِينَ، دَ تَڧُواْنَ تُرَارٜىٰ غَ وَطَنْسُ أَلُّواْلِ، دَ تَيِنْ سُجَّدَ غَ غُمَكَ، عَيْكِنْ حَنُّوَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zan hurta hukuncin da zan yi musu saboda dukan muguntarsu, da suka bar bina, suka ƙona turare ga gumaka, suka kuma bauta wa gumakan da suka yi.