Jeremiah 1:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Kafin in siffanta ka a cikin ciki na san ka, kafin a haife ka, na keɓe ka; na naɗa ka ka zama annabi ga al’ummai.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«تُنْ كَاڢِنْ إِنْ صِڢَّتَاكَ عَثِكِنْ ثِكِ، نَسَنْكَ، تُنْ كَاڢِنْ أَحَيْڢٜىٰكَ، نَكٜىٰٻٜىٰكَ؞ نَنَطَكَ أَنَّبِے غَ أَلْعُمَّيْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Na san ka tun kafin a yi cikinka, Na keɓe ka tun kafin a haife ka, Na sa ka ka zama annabi ga al'ummai.”