Jeremiah 11:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sun koma ga zunuban kakanni kakanninsu, waɗanda suka ƙi su saurari maganata. Suka bi waɗansu alloli don su bauta musu. Da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda duk sun take alkawarin da na yi da kakanni kakanninsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُنْ جُويَا غَ عَيْكَتَ لَيْڢُواْڢِنْ كَاكَنِّنْسُ وَطَنْدَ سُكَڧِ بِيَيَّ دَ مَغَنَاتَ؞ سُو مَا سُكَبِے وَطَنْسُ أَلُّواْلِ سُكَيِ مُسُ سُجَّدَ؞ غِدَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ دَ نَ يَهُودَ سُنْ كَرْيَ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَتَ وَدَّ نَيِ دَ كَاكَنِّنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sun koma a kan laifofin kakanninsu, waɗanda suka ƙi jin maganata, suka bi gumakansu don su bauta musu, jama'ar Isra'ila da na Yahuza sun ta da alkawarina wanda na yi da kakanninsu.