Jeremiah 11:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Garuruwan Yahuda da mutanen Urushalima za su tafi su yi kuka ga allolin da suke ƙona wa turare, amma ba za su taimake su ba sam sa’ad da masifar ta auku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً مُتَنٜىٰنْ غَرُضُوً يَهُودَ دَ مَذَوْنَنْ عُرُوشَلِيمَ ذَاسُ تَڢِے سُيِ كُوكَا غَ أَلُّواْلِنْسُ وَطَنْدَ سُكٜىٰ ڧُواْنَ مُسُ تُرَارٜىٰ؞ عَمَّا أَلُّواْلِنْ بَذَاسُ عِيَ ثٜىٰتُوانْسُ أَ لُواْكَثِنْ وَهَلَرْسُبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan biranen Yahuza da mazaunan Urushalima za su tafi, su yi kuka ga gumaka waɗanda suka ƙona musu turare, amma ba za su iya cetonsu a lokacin wahalarsu ba.