Jeremiah 11:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji Maɗaukaki, wanda ya dasa ki, ya furta miki masifa, domin gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda sun aikata mugunta suka kuma tsokane ni in yi fushi ta wurin ƙona wa Ba’al turare.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«نِے يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا وَنْدَ نَدَسَكُ، نَيَنْكٜىٰ شَوَرَا ثٜىٰوَ مَسِيڢَ ذَاتَ ڢَاطُواْ مُكُ، سَبُواْدَ مُغُنْتَارْ دَكُكَ عَيْكَتَ، يَا كُو غِدَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ دَ نَ يَهُودَ؞ غَمَا كُنْسَا نَيِ ڢُشِے سَبُواْدَ كُنْ ڧُواْنَ تُرَارٜىٰ غَ بَعَلْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji Mai Runduna, wanda ya dasa ku, ya hurta masifar da za ta same ku saboda muguntar da mutanen Isra'ila da na Yahuza suka yi, suka tsokane ni in yi fushi saboda suna ƙona wa Ba'al turare.