Jeremiah 12:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
’Yan’uwanka, iyalinka har su ma sun bashe ka; sun tā da kuka mai ƙarfi a kanka. Kada ka amince da su, ko da yake suna faɗa maganganu masu kyau game da kai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا حَرْ یَنْعُوَنْكَ دَ غِدَنْ مَحَيْڢِنْكَ سُنْثِ أَمَانَرْكَ، سُنَ إِيهُ سُنَ ڢَرَوْتَرْكَ؞ كَدَ كَأَمِنْثٜىٰ دَسُو، كُواْ دَ سُنْيِ مَكَ مَغَنَ مَيْ دَاطِے؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama har da 'yan'uwanka da gidan mahaifinka, Sun ci amanarka, Suna binka da kuka, Kada ka gaskata su, Ko da yake suna faɗa maka maganganu masu daɗi.”