Jeremiah 13:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Waɗannan mugayen mutane, waɗanda suka ƙi saurari maganata, waɗanda suka biye wa taurin zuciyarsu suka bi waɗansu alloli don su bauta su kuma yi musu sujada, za su zama kamar wannan abin ɗamara gaba ɗaya marasa amfani!
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُوغُوَرْ جَمَعَرْ نَنْ تَڧِے جِنْ مَغَنَاتَ؞ تَنَ بِنْ تَوْرِنْ ذُوثِيَارْتَ، حَرْ تَبِے وَطَنْسُ أَلُّواْلِ تَنَ بَوْتَا مُسُ تَنَيِ مُسُ سُجَّدَ؞ ذَاتَ ذَمَ كَمَرْ وَنَّنْ أَبِنْ طَمَرَ، وَنْدَ بَاشِ دَ أَمْڢَانِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wannan muguwar jama'a, wadda ta ƙi jin maganata, wadda ta taurare, ta bi son zuciyarta, ta kuma bi gumaka ta bauta musu, ta yi musu sujada, za ta zama kamar abin ɗamaran nan, wanda ba shi da sauran amfani.