Jeremiah 14:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ga abin da Ubangiji ya ce game da wannan mutane, “Suna son yawace-yawace ƙwarai; ba sa hana ƙafafunsu yawo. Saboda haka Ubangiji bai yarda da su ba; yanzu zai tuna da muguntarsu zai kuma hukunta su saboda zunubansu.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا أَبِنْدَ يَهْوٜىٰهْ يَڢَطَا غَمٜىٰدَ جَمَعَرْ نَنْ، «حَڧِيڧَ سُنَ سُواْ سُيِ تَيَٰوُاْ، حَنْكَلِنْسُ بَ أَوُرِے طَيَ يَكٜىٰبَ؞ سَبُواْدَ حَكَ، نِے يَهْوٜىٰهْ بَنْ كَرْٻٜىٰسُبَ، يَنْذُ ذَنْ تُنَ دَ لَيْڢُواْڢِنْسُ، إِنْ حُكُنْتَسُ دُواْمِنْ ذُنُبَنْسُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Haka Ubangiji ya ce a kan waɗannan mutane, “Sun cika son yawaceyawace, ba su iya zama wuri ɗaya, don haka ni Ubangiji, ban yarda da su ba, zan tuna da laifofinsu in hukunta zunubansu.”