Jeremiah 14:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Manyan mutane suna aika bayinsu su ɗebo ruwa a maɓulɓulai amma babu ruwa. Suka dawo da tulunansu haka nan; da kunya da kuma ƙasƙanci, da kawunansu a rufe.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مَنْيَنْ مُتَنٜىٰنْ عُرُوشَلِيمَ سُنْ عَيْكَ بَايِنْسُ نٜىٰمَنْ ضُوَ؞ بَايِنْ سُكَ تَڢِے رِجِيُواْيِ، بَسُ كُوَ سَامِ ضُوَبَ، سُكَ كُواْمَ دَ تُلُنَنْسُ وُاْڢِ؞ كُنْيَا دَ ڧَسْڧَنْثِ سُكَ رُڢٜىٰسُ، سُكَ رُڢٜىٰ ڢُسْكَرْسُ سَبُواْدَ كُنْيَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Manyan mutanenta sun aiki barorinsu su ɗebo ruwa. Da suka je maɓuɓɓuga, sai suka tarar ba ruwa. Sai suka koma da tulunansu haka nan, An kunyatar da su, an ƙasƙantar da su, Suka lulluɓe kansu don kunya.