Jeremiah 15:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ban taɓa zauna a cikin ’yan tawaye ba, ban taɓa yi murna da su ba; na zauna ni kaɗai domin hannunka yana a kaina ka kuma sa na cika da haushi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَنْ ذَوْنَ ثِكِنْ مَاسُيَوَنْ سُوانْ جِنْ دَاطِے بَ، بَنْ كُوَيِ رَايُوَرْ مُرْنَ تَرٜىٰدَسُوبَ؞ نَا ذَوْنَ نِے كَطَيْ، غَمَا حَنُّنْكَ مَيْ بِدَنِ يَنَ عَكَيْنَ، كَسَا نَثِكَ دَ ڢُشِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ban zauna cikin ƙungiyar masu annashuwa ba. Ban kuwa yi murna ba, Na zauna ni kaɗai saboda kana tare da ni, Gama ka sa na cika da haushi.