Jeremiah 15:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
In kuma suka tambaye ka, ‘Ina za mu tafi?’ Sai ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Waɗanda aka ƙaddara ga mutuwa, ga mutuwa za su; waɗanda aka ƙaddara ga takobi, ga takobi za su; waɗanda aka ƙaddara ga yunwa, ga yunwa za su; waɗanda aka ƙaddara ga zaman bauta, ga zaman bauta za su.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِدَنْ كُمَ سُكَ تَمْبَيٜىٰكَ، ‹إِنَا ذَامُ تَڢِے؟› كَثٜىٰ مُسُ، ‹غَا أَبِنْدَ نِے يَهْوٜىٰهْ نَثٜىٰ؞› « ‹دُكْ وَنْدَ عَكَ ڧَدَّرَ وَبَلَعِ، مُتُوَرْ بَلَعِ ذَيْ يِ! دُكْ وَنْدَ عَكَ ڧَدَّرَ وَتَكُواْبِے، مُتُوَرْ تَكُواْبِے ذَيْ يِ! دُكْ وَنْدَ عَكَ ڧَدَّرَ وَيُنْوَ، مُتُوَرْ يُنْوَ ذَيْ يِ؞ دُكْ وَنْدَ عَكَ ڧَدَّرَ وَبَوْتَا، بَوْتَا ذَيْ يِ!›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da suka tambaye ka, ‘Ina za mu tafi?’ Sai ka faɗa musu cewa, Ubangiji ya ce, ‘Waɗanda suke na annoba, su tafi ga annoba! Waɗanda suke na takobi, su tafi ga takobi! Waɗanda suke na yunwa, su tafi ga yunwa! Waɗanda suke na bauta, su tafi ga bauta!’