Jeremiah 16:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai ka ce musu, ‘Wannan ya zama haka domin kakanninku sun rabu da ni,’ in ji Ubangiji, ‘suka bi waɗansu alloli suka kuma bauta musu. Suka rabu da ni, ba su kuwa kiyaye dokata ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ كَثٜىٰمُسُ، ‹نِے يَهْوٜىٰهْ نَا يِوَنَّنْ سَبُواْدَ كَاكَنِّنْكُ سُنْڧِينِ، سُنْ كُمَبِے وَطَنْسُ أَلُّواْلِ، سُنْيِ مُسُ سُجَّدَ، سُنْيِ مُسُ بَوْتَا؞ سُنْڧِينِ بَسُ كُوَ كِيَايٜىٰ كُواْيَرْوَاتَابَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ka faɗa musu cewa, Ubangiji ya ce, ‘Domin kakanninku sun rabu da ni, sun bi gumaka, sun bauta musu, sun yi musu sujada. Sun rabu da ni, sun ƙi kiyaye dokokina.