Jeremiah 16:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka zan fitar da ku daga wannan ƙasa zuwa wata ƙasar da ku da kakanninku ba ku taɓa sani ba, a can kuwa za ku bauta wa waɗansu alloli dare da rana, gama ba zan nuna muku tagomashi ba.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ، ذَنْ جٜىٰڢَرْ دَكُو وَجٜىٰ دَغَ وَنَّنْ ڧَسَا ذُوَا وَتَ ڧَسَا، ڧَسَرْدَ كُواْ كُو كُواْ كَاكَنِّنْكُ بَكُسَنْتَبَ؞ أَوُرِنْ ذَاكُ بَوْتَاوَ وَطَنْسُ أَلُّواْلِ دَرٜىٰ دَ رَانَ، غَمَا نِے بَذَنْ نُونَ مُكُ جِنْڧَيْبَ؞ نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Don haka zan fitar da ku daga wannan ƙasa zuwa wata ƙasa wadda ku ko kakanninku ba ku sani ba. A can za ku bauta wa gumaka dare da rana, gama ba zan nuna muku ƙauna ba.’