Jeremiah 16:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
amma za su ce, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fitar da Isra’ilawa daga ƙasar arewa da kuma daga dukan ƙasashe da ya kora su.’ Gama zan komo da su zuwa ƙasar da na ba wa kakanninsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ مَيْمَكُوانْ حَكَ ذَاعَ ثٜىٰ، ‹نَا ضَنْڟٜىٰ دَ سُونَنْ يَهْوٜىٰهْ مَيْ رَيْ، وَنْدَ يَڢِتَرْدَ إِسْرَٰٓءِيلَ دَغَ ڧَسَرْ أَرٜىٰوَ دَ دُكَنْ ڧَسَاشٜىٰنْدَ يَوَرْوَاڟَرْ دَسُو؞› غَمَا ذَنْ كُواْمُواْ دَسُو ذُوَا ڧَسَرْسُ وَدَّ نَبَا كَاكَنِّنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma za a ce, ‘Na rantse da Ubangiji wanda ya fito da jama'ar Isra'ila daga ƙasar arewa, da kuma daga dukan ƙasashe da ya kora su,’ gama zan komo da su zuwa ƙasar da na ba kakanninsu.