Jeremiah 16:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zan riɓaɓɓanya sakayyar da zan yi musu saboda muguntarsu da zunubinsu, domin sun ƙazantar da ƙasata da ƙazantattun gumakansu marasa rai, suka kuma cika abin gādona da gumakansu na banƙyama.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَنْ حُكُنْتَسُ دَ ثِكَكّٜىٰنْ حُكُنْثِ ڠُورْڠُودُوانْ لَيْڢُواْڢِنْسُ دَ ذُنُبَنْسُ، غَمَا سُنْ ڧَظَنْتَرْدَ ڧَسَاتَ تَوُرِنْ غُمَكَنْسُ مَرَسَ رَيْ مَاسُ ڧَظَنْتَا؞ سُنْ كُمَ ثِكَ ڧَسَاتَ دَ أَبُبُوَ بَنْ ڨَمَ، ڧَسَرْدَ تَكٜىٰ أَبِنْ غَادُواْنَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zan riɓaɓɓanya sakayyar da zan yi musu saboda muguntarsu da zunubinsu, domin sun ƙazantar da ƙasata da ƙazantattun gumakansu marasa rai, abin gādona kuma sun cika shi da abubuwansu na banƙyama.”