Jeremiah 17:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi. Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo; ganyayensa kullum kore suke. Ba shi da damuwa a shekarar fări ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَنَ كَمَ دَ إِتَاثٜىٰ وَنْدَ عَكَ دَسَ كُسَدَ ضُوَ، وَنْدَ يَمِيڧَ سَيْوُاْيِنْسَ ثِكِنْ ضُوً؞ بَذَيْجِڟُواْرُوانْ ذَاڢِنْ رَانَ بَ، غَنْيٜىٰنْسَ بَاسَ بُوشٜىٰوَ؞ بَايَ جِنْ ڟُواْرُوانْ لُواْكَثِنْ رَشِنْ ضُوَ، بَايَ كُمَ دَيْنَ بَادَ یَیَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Shi kamar itace ne wanda ake dasa a bakin rafi Wanda yake miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafin, Ba zai ji tsoron rani ba, Kullum ganyensa kore ne, Ba zai damu a lokacin fari ba, Ba zai ko fasa yin 'ya'ya ba.